OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwankwaso Ya Nada Daurawa Limancin Sabon Masallacin Sa

Kwankwaso Ya Nada Daurawa Limancin Sabon Masallacin Sa

2023 Presidency: Many APC Lawmakers are joining Senator Rabi'u Musa Kwankwaso in the NNPP

Tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya nada Malam Aminu Ibrahim Daurawa Limamin Masallacin juma'ar da ya gina a gidansa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da gidauniyar Kwankwasiyya ta fitar a jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce an nada Daurawa ne tare da wasu Malamai 7 a matsayin limamai da mataimaka.

 Idan za a iya tunawa a ranar Juma'ar da ta gabata ne Kwankwaso ya kaddamar da sabon masallacin da ya kyautar ga al'ummar musulmi baki daya.

Sanarwar takara da cewa wadanda aka nada din sun hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin babban Limami.

 Sai Sheikh Sadiq Isa Abdullahi da Sheikh Gwani Baffa Ite da kuma Sheikh Bazallah Nasir Kabara a matsayin limamai.

Sauran sun hada da Dr. Sani Ashir a matsayin Yan kwamitin masallacin, da Dr Muhammad Khamis Hussain a matsayin Sakatare.

Sai Sheikh Nura Abdullahi Salihu a matsayin dan Majalisa da kuma Malam Ashir Nata’ala limamin kamsusalawat.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci