OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jigawa: Adadin wadanda ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar su ya kai 108

Jigawa: Adadin wadanda ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar

Daga jihar Jigawa, adadin wadanda ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar su daga watan Agusta ya zuwa yanzu ya Kai 108.

Ku tuna cewa AllNews Hausa ta ruwaito cewa adadin ya kai mutum 98 a baya sai dai yanzu lissafin ya haura. 

Kamar yadda rundunar 'yan sandan Jihar Jigawa ta bakin mai magana da yawun ta, Lawan Adam ya bayyana, yawancin wadanda suka mutu sun mutu ne ta hanyar nutsewa, tsawa, da kuma rugujewar gine-gine.

A cewar Adam, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, mutane 108 ne yanzu suka rasa rayukan su wanda hakan ke nuna karuwar adadin.

Ku tuna cewa gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru ya fice ƙasar waje domin hutu yayin da hakan ke faruwa.

Lamarin wanda yasa mutane suka soke shi don nuna rashin jin dadin tafiyar tasa a lokacin da jama'ar sa ke fama da iftila'in ambaliyar ruwa. 

Gwamnan ya dawo daga hutun ne makonni biyu da tafiyar tasa a ranar Jumma'a da ta gabata. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci