OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jam'iyyar NNPP ta nemi a gurfanar da shugaban jam'iyyar APC da aka kama da katunan zabe

Jam'iyyar NNPP ta nemi a gurfanar da shugaban jam'iyyar APC

Jamiyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kungiyoyin farar hula a karkashin inuwar Alliance for Good Governance sun bukaci da a gaggauta gurfanar da wani jigo a jamiyyar APC, Aliyu Shana, da aka kama da katin zabe kimanin guda 300 a Kano.

 

Mista Shana, wanda shi ne shugaban jamiyyar APC na gundumar Yautan Arewa, karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano, a ranar Jumaar da ta gabata ne yan sanda suka cafke shi zuwa hedikwatar rundunar domin yi masa tambayoyi.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa mallakar katin zabe na wasu ba bisa kaida ba ya sabawa sashe na 21 da 22 karamin sashe na 1 (a), (b) da (c) na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

 

 

A wata sanarwa da shugaban NNPP na jihar Umar Doguwa ya fitar, ya ce jamiyyar ta umurci tawagar lauyoyin ta da su kuma shigar da kara a kan wanda ake zargin da kuma masu daukar nauyinsa.

 

"Na umarci mai ba mu shawara kan harkokin shari'a da ya rubuta wa Hukumar zabe (INEC) don a bibiyi matakin da ya dace a kan lamarin," in ji Mista Doguwa.

 

Ya ce batun tara katin zaben jama'ana ya zama babban abin damuwa a jihar Kano musamman ga zabe mai gabatowa a 2023.

 

An tabbatar da wannan kamen, muna nan muna jiran matakin da hukumar zabe mai zaman kanta da yan sandan Najeriya za su dauka,inji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci