APC
Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa a ranar Asabar ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da ita daga tsayar da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jihar.
Wata babbar kotun tarayya da ke Yola a ranar Juma’a ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka yi a jihar.
Jam’iyyar ta zabi Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka soke wanda ya gudana a ranar 26 ga watan Mayu.
Ta samu kuri’u 430 inda ta doke abokin hamayyarta Nuhu Ribadu wanda ya samu kuri’u 288.
Alkalin kotun, Abdulaziz Anka, ya ki amincewa da rokon da jam’iyyar ta yi na sake gudanar da sabon zaben fidda gwani, wanda hakan ke nufin jam’iyyar ba za ta samu dan takara a zaben ba.
Mista Ribadu dai ya garzaya kotu ne bisa zargin rashin bin ka’ida wajen gudanar da zaben fidda gwani.
Kotun ta ce zaben fidda gwanin an gudanar da shi ne ba tare da bin ka’idar zaben 2022, kundin tsarin mulkin Najeriya, da ka’idojin jam’iyya ba.
Alkalin ya ce zaben Misis Binani ya sabawa sashe na 85 na dokar zabe saboda an yi karin kuri'u a lokacin zaben fidda gwanin.
Da yake magana a wani taron manema labarai a ranar Asabar, sakataren jam’iyyar APC na jihar, Raymond Chidama, ya roki magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, ya ce jam’iyyar za ta daukaka kara kan hukuncin.
Ya ce bayan yanke hukuncin ne shugabannin jam’iyyar na jihar suka yi taro inda suka amince su dawo su kalubalancin hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara.
0 Tsokaci