OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Zaben fidda gwannin Ondo: Dan takara Ariyomo ya taya Aiyedatiwa da yayi nasara murna

Zaben fidda gwannin Ondo: Dan takara Ariyomo ya taya Aiyedat

Engr. Tunji Light Ariyomo, dan takarar da aka cire shi daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC sakamakon matsalolin cikin gida da ke tsakanin kwamitin shirya zabe na jam’iyyar APC da sakataren kungiyar na kasa kan tsawaita sayar da fom, ya taya Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa, wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Ondo murna. 

 

Ariyomo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ariyomo wanda ya biya kudin takara da fam miliyan 50 da ake bukata domin tsayawa takarar zaben fidda gwani a ranar Juma’a 5 ga Afrilu, 2024, amma ba a taba tantance shi ba saboda ofishin sakataren kungiyar na kasa bai amince da karin kwanaki 2 da Felix Morka, mai magana da yawun jam’iyyar ya fitar, wanda ya sanar da tsawaita wa’adin ranar Alhamis 4 ga Afrilu, 2024 a wata sanarwa da aka buga wanda har yanzu ba a janye ba.

 

"Da aka tambaye shi ko zai kai karar jam'iyyar saboda cirewar, Ariyomo ya amsa da cewa "ko kadan. Ni, Olatunji Ariyomo, ba zan kawo cikas ga tsarin da aka kammala cikin nasara ba hasali ma ina taya wanda ya yi nasara, Hon. Aiyedatiwa murna" 

 

“Ya kara da cewa Gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa ya lashe wannan zagaye na zaben, Yakamata jam'iyyar ta yi shirin tukarar babban zabe mai zuwa.

 

 Ariyomo ya ci gaba da cewa, "Na yarda cewa har yanzu ba mu fara yin zaben fidda gwanni irin na kasar Amurka ba amman har yanzu ina fatan hakan zai faru a nan gaba, Na kuma yarda cewa ba za mu iya samun nau'in sakamakonsu daga irin tsarinmu ba. Amma duk wanda ke cikin wannan zaben a wannan ranar ya san da hakan saboda haka fatana shine a sasanta juna domin zaben Nuwamba yana dada karatowa"

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci