OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar kula da asibitocin ta jihar Kano ta raba magunguna da darajar su ta kai N5m

Hukumar kula da asibitocin ta jihar Kano ta raba magunguna d

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta ware magunguna da kayan aiki da kudinsu ya kai Naira 5,317,387.50 ga dukkanin manyan hukumomin lafiya dake jihar.

 

Babban sakataren hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abubakar Yusuf Labaran ya jagoranci rabon kayyakin da aka gudanar a Kano ranar Talata.

 

Nagoda yace sun tanadi magungunan da kayayyakin amfani domin ayiwa marasa lafiya amfani da su musamman don kula da wadanda hatsari ya shafa da mata masu juna biyu, maimakon a ajiye su a guri guda.

 

Ya kuma gargadi shugabannin asibitocin da ma'aikatan da su guji siyarwa, ko karkatar da magungunan da aka kawo. Hakazalika, ya jaddada ci gaba da sa ido kan yanayin amfani da ƙwayoyi don tabbatar da marasa lafiya sunci gajiyar shirin.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci