OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Makonni da suka shude

Gwamnatin Zamfara ta gano bullar wata bakuwar cuta

Gwamnatin Zamfara ta gano bullar wata bakuwar cuta

Dakta Hussaini Anka, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko a jihar Zamfara, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gano bullar wata  bakuwar cuta da ba a san ta ba a kananan hukumomi biyu a jihar.

Anka ya bayyana cewa an aike da tawagar ma’aikatan lafiya domin gudanar da bincike kan cutar a kananan hukumomin Maradun da Shinkafi, musamman a kauyukan da ke kusa da jihar Sakkwato.

 A wata zantawa da manema labarai a Gusau, Anka ya bayyana cewa tun da suka samu rahoton bullar cutar ya sanda an dauki matakin gaggawa. An tattara samfuran ruwa, jini, fitsari, da sauran samfuran da suka dace daga wuraren da abin ya shafa kuma an aika da su don gwadawa.

Anka ya kara da cewa "Mun samu sakamakon gwajin da akayi kuma mun ziyarci kauyukan da lamarin ya shafa domin mu'amala da wadanda suka kamu da cutar, bisa ga binciken da muka yi, cutar ta na sanya hantar mutum ta kumbura hakan yasa mike zargin gurbatatten ruwa ne yayi sanadin ta"

Ya ce wasu daga cikin matakan gaggawa da aka dauka shi ne na hana wadanda abin ya shafa shan gurbataccen ruwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci