OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Harin Jirgin Kasa: El-Rufa'i Ya Ba Wa Iyalan Fasinjojin da Suka Rasu N2m kowanne

Harin Jirgin Kasa: El-Rufa'i Ya Ba Wa Iyalan Fasinjojin da S

Governor Nasir El-Rufa'i of Kaduna state| Photo Source: PM News

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya jajantawa iyalan mutane 9 da aka kashe a harin jirgin kasa na Kaduna.

Gwamnan ya bai wa iyalan kowannen su Naira miliyan biyu domin jajanta musu bisa wannan mummunan lamari da ya faru a ranar Litinin 28 ga watan Maris na 2022.

Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KAD-SEMA), Mohammed Muazu Mukkadas ne ya bayyana hakan.

Mukkadas wanda ya gabatar da kudaden ga iyalan ya kuma mika kudi naira 250,000 kowannen su ga wadanda suka jikkata da raunuka daban-daban a yayin harin.

Wadanda abin ya shafa wanda adadin su ya kai 22 sun karbi kudin ne bayan da gwamnatin jihar ta biya musu kudaden jinya a asibiti.

Mukkadas ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kuma iyalan wadanda suka mutu wanda suke cikin yanayin jimami.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin sa, sakataren ya bayyana cewa hukumar ta amsa kira cikin gaggawa domin bayar da taimako tare da hadin kan sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa a yayin harin.

Ya ce, “Lokacin da muka samu kiran, mun samu motocin daukar marasa lafiya da motocin bas don kwashe su, mun kwashe wadanda aka kashe da wadanda suka samu munanan raunuka da Wanda ya tsere muka ajiye su a Asibitin Sojoji na 44 da Asibitin Saint Gerard.”

Ya kara da cewa gaggawar da hukumar ta bayar ya samar da cibiyar kiran gaggawa da ta baiwa iyalan wadanda lamarin ya shafa su nemi bayanai.

Da yake bayyana tallafin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce, “Kuma a jiya Talata 19 ga watan Afrilu na 2022, Gwamna Nasir El-Rufa'i ya nuna tausayi ya amince da raba kudade (N2m kowanne) ga magadan mutane 9 da suka mutu, da N250,000 kowanne zuwa 22 da suka samu munanan raunuka, wanda hakan taimako ne da ake nufi don rage musu radadi."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci