OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Tarayya tana biyan kudin tallafin daya zarta na baya - El rufai

Gwamnatin Tarayya tana biyan kudin tallafin daya zarta na ba

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce a halin yanzu gwamnatin tarayya na biyan tallafin man fetur fiye da na baya. 

 

El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kammala gabatar da mukala a wani taron karawa juna sani kan inganta kwarewar jami’an gwamnati wajen aiwatar da manufofi da kuma samar da ingantacciyar hanyar yin aiki da alumma ga masu rike da mukaman siyasa a Maiduguri a ranar Litinin. 

 

A cewarsa, a halin yanzu gwamnatin tarayya na cigaba da bayar da tallafin man fetur duk da haka, sanar da cire tallafin da farko.

 

"A ko yaushe ina goyon bayan janye tallafin man fetur amma a yayin aiwatar da manufofin, gwamnati ta fahimci cewa dole ne a dawo da tallafin, a halin yanzu, gwamnati na kashe makudan kudade wajen bayar da tallafi, har ma fiye da yanda yake a da" inji El rufai.

 

Ya kara da cewa "Ya kamata ku zama masu aiki da hankali. Duk lokacin da kuka tsara manufofin, kuka fara aiwatar da shi, kuma da alama baya aiki yanda ya dace ya kamata ku kasance masu tawali'u ku ce wannan abun ba ya aiki, kuma ku samar da gyaran daya dace". 

 

Idan zaku iya tunawa Shugaba Tinubu a ranar rantsar da shi ya bayyana cire tallafin man fetur a kasar nan. Saidai wasu bayyanai sun tabbatar da gwamnatin tarayya ta cigaba da biyan tallafin ta bayan gida.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci