OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Peter Obi Ya Caccaki El-Rufai, Yace Bai Taba Bada Umarnin Kama Shi Ba

Peter Obi Ya Caccaki El-Rufai, Yace Bai Taba Bada Umarnin Ka

Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan maganar da ya yi cewar ya taba sa a kamashi a jihar Anambra a shekarun baya.

 

El-Rufai, a wani taron tattaunawa da kungiyar hadin gwiwa ta Arewa ta shirya a Kaduna ranar Litinin, ya yi ikirarin cewa an taba tsare shi shekaru tara da suka gabata a jihar Anambra na tsawon saoi 48 bisa umarnin Mista Obi.

 

A shekarar 2013 na je jihar Anambra a matsayin jamiin jamiyyar APC domin shaida zaben fidda gwani na gwamna da za a yi a wancan lokacin, Peter Obi a lokacin yana gwamna, ya sa aka kama ni inda aka tsare ni na tsawon saoi 48 a dakina na otal,cewar Gwamnan Kaduna.

 

Yanzu a matsayinsa na Gwamna El-Rufai ya ce yana da dukkan karfin iko da zai tunkari dan takarar jamiyyar LP amma ba zai yi hakan ba saboda kasancewr sa dan Arewa.

A nasa bangaren, Obi ya bayyana kalaman gwamna El-Rufa'i a matsayin wani abinda bai kamata a fito fili ana yada shi ba.

 

Abin da mai girma Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya fada game da ni ya jawo hankalina.Muna girma nauyi na kara hawa kan mu,a wannan gabar ya kamata ace mu dinga hangen nesa,kuma mudinga tauna kalaman mu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci