OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnati Ce Ke Da Alhakin Jin Koken Iyayen Ɗalibai - ASUU

Gwamnati Ce Ke Da Alhakin Jin Koken Iyayen Ɗalibai - ASUU

Ƙungiyar Malaman jami'oi ta kasa, ASUU ta shawarci iyayen ɗalibai dasu miƙa koken su ga gwamnatin tarayya domin kawo karshen yajin aiki jami'oi da ya shafe tsawon wata shida yana gudana a fadin Najeriya.

A yayin wata hira da manema labarai a ranar Asabar, shugaban hukumar ta kasa, farfesa Emmanuel Osodoke ya ce, gwamnatin tarayya ce kawai ke da alhakin jin koken iyayen dalibai ta hanyar cika alkawuran da ta yiwa ƙungiyar.

Osodoke ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ke biyan malaman makarantu, saboda haka ita ya kamata iyayen dalibai su tunkara da koken su na kawo karshen yajin aiki, domi ASUU, bata da hurumin yin haka.

Bayanin shugaban ƙungiyar malaman jami'oin ta kasa, ya bayyana ne biyo bayan kira da ministan ƙwadago yayi ga iyayen dalibai da su roki kungiyar ta ASUU, domin ta dakatar da yajin aiki da suke a fadin kasa.

Idan ba a manta ba, Kungiyar malaman jami'oi ta ASUU, ta tsunduma yajin a aikin sai baba ta gani ne tun ranar 14 ga watan Fabarairu na shekarar da muka ciki, kimanin watanni shida kenan zuwa yanzu.

Gwamnati ta kafa kwamiti wanda tattauna da kungiyar, tare da kawo karshen yajin aikin da ya-ƙi-ci ya-ƙi cinyewa amma har yanzu ba'a cimma hakan ba.

A halin yanzu, gwamnati ta kara naɗa wani kwamiti karkashin jagorancin ministan sadarwa da cigaban tattalin arziki, farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami domin warware matsalar dake tattare da hanyar biyan kuɗaɗen malamai wacce gwamnati ta tanada, IPPIS. 

Sai dai kungiyar ASUU, tace yin hakan ba zai magance matsalar ba, sai dai a bi hanyar da ta tanada don biyan kudaden ƴaƴan ta, mai suna UTAS.

VAN/LA

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci