OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Davido ya sanar da ya kusa daina waka baki daya

Davido ya sanar da ya kusa daina waka baki daya

Shahararren mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana a ranar Alhamis cewa ba zai sake fitar da waka ba bayan ya kammala wannan album din.

 

Idan dai za a iya tunawa, Davido ya yi ta yawo a kafafen yada labarai a kwanan baya kan fadan sa ta yanar gizo da mawaki Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid. 

 

A wata wallafa da yayi a kafafen sa na sada zumunta yace akwai wasu da suka shirya makarkashiyar ganin bayansa.

 

Ya wallafa a shafinsa na X "daga album din nan zan daina waka baki daya tunda naga akwai mutane da suka kagu suga sun fitar dani daga masana'antar"

 

Mawakin a ranar Laraba ya fitar da fefen bediyon wakarsa mai suna "Kante" da suka raira tare da mawakiya Fave.

 

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci