OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Daraktan NYSC ya hori masu yiwa kasar hidima su guji yin tafiyar dare

Daraktan NYSC ya hori masu yiwa kasar hidima su guji yin taf

Shugaban Hukumar dake lura da masu yi wa kasa hidima, NYSC Birgediya Janar Y.D. Ahmed ya gargadi matasan da su guji yin tafiyar dare haid da mutunta al'adun wuraren da aka kaisu domin hidimtawa kasar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin yaye su daga sansanin horo da aka gudanar a ranar Talata a jihar Sokoto. 

Janar Ahmed wanda ya samu wakilcin kodinetan NYSC, Alhaji Usman Yakubu Yaro, ya jaddada mahimmancin tsaro, sannan ya bukaci ‘yan kungiyar su guji tafiye-tafiye da daddare saboda tabbatar da tsaro.

Yace "da karfe 6:00 na yamma tayi toku dakatar da tafiyar ku, ku nemi masaukin da zaku kwana.Ina yi muku gargaɗi da ku kiyaye kimar kishin ƙasa, himma, da jajircewa, halaye ne masu muhimmanci na gina ƙasa." 

Ya kuma shawarci matasan da su mutunta al’adun mutanen da suke zaune a yankunansu.

Janar Ahmed ya kara da kwadaitar da ‘yan bautar kasar da su ci gaba da maida hankali kan shirin samar da koyar da sanaoin dogaro da kai da bunkasa kasuwanci wato SAED.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci