OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Tarayya ta bawa masu POS wa'adin yin rajista da hukumar CAC

Gwamnatin Tarayya ta bawa masu POS wa'adin yin rajista da hu

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da harkokin kamfanoni, CAC, ta baiwa kamfanonin PoS, wa’adin watanni biyu su yi rajistar wakilansu da ‘yan kasuwa. 

 

Wannan matakin dai ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin Babban Bankin Najeriya.

 

 Babban magatakardar hukumar ta CAC Hussaini Ishaq Magaji a Abuja a ranar Litinin ya sanar da hakan ne bayan wata ganawa da wasu kamfanonin Fintechs.

 

Akwai akalla masu PoS sama da miliyan 1.9 a faɗin ƙasar, nan wannan rajistar zata kiyaye kasuwancin ƙarƙashin sashe na 863 (1) na Dokar Kamfanoni da Allied Matters, CAMA 2020 da ka'idojin CBN na 2013.

 

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce, “Hukumar kula da harkokin kamfanonin fintech a Najeriya, wadanda aka fi sani da masu PoS sun amince da wa’adin watanni biyu na yin rajistar wakilansu, ‘yan kasuwa, da daidaikun mutane da hukumar ta CAC bisa ga ka’idojin doka da oda.An cimma yarjejeniyar ne a yau yayin wani taro da aka yi tsakanin Fintechs da babban magatakardar hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji, a Abuja.”

 

 Wa’adin rajistar wanda zai kare a ranar 7 ga Yuli, 2024, an yi shi ne don kare ‘yan kasuwa. Masu sana'ar sun yi alƙawarin yin haɗin gwiwa tare da Hukumar don tabbatar da aiwatar da umarnin ba tare da matsala ba.

 

Wannan sabon umarnin ya zo a kan abubuwan da suka faru na zamba akai-akai da suka shafi tashoshin POS da kuma shirye-shiryen dakatar da cinikin cryptocurrency.

 

A makon da ya gabata, CBN ya dakatar da manyan kamfanonin fintech kamar Kuda, Opay, PalmPay da Moniepoint daga rajistar sabbin kwastomomi tare da umurtarsu da su gargadi abokan cinikinsu game da cinikin cryptocurrency tare da yin barazanar toshe duk wani asusun da aka samu yana yin irin waɗannan ayyukan. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci