OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta jaddada hukuncin bayar da damar kama Yahaya Bello

Kotu ta jaddada hukuncin bayar da damar kama Yahaya Bello

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta zargi tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa yunkurin gujewa shari’ar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shigar a kansa.

 

Kotun, a hukuncin da mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar a ranar Juma’a, ta sake jaddada umarnin da ta bayar a ranar 17 ga watan Afrilu, wanda ya umurci hukumomin tsaro da su kama shi tare da gurfanar da shi a gabanta domin amsa tuhume-tuhume 19 da ake yi masa.

 

Mai shari'ar yace guduwa da buyan da Yahya Bello yayi yayin da aka fara sauraron kara akan tuhumar da ake masa a gaban kotun ya nuna tsantsan raini da rashin girmama kotu.

Yana mai jaddada cewa ya kamata ya ba da kansa a lokacin da ya fahimci umarnin kama shi da aka yi. "Doka ta yanke shawarar cewa wanda ya ki bin umarnin kotu kuma ya nuna rashin girmamawa ga kotu ba zai iya tsammanin sassauci a hukuncin kotun ba. Abun da wanda wanda ake tuhuma ya kamata yayi shi ne ya bi umarnin kotu ta hanyar mika Kansas ga jamian tsaron ya kuma bayana a gaban kotun.

 

“Sashe na 287 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wand aka yi wa kwaskwarima, ya umurci dukkan mutane da su bi dukkan umarnin kotu"

 

Dokar tace "masu ikon aiwatar da umarnin kotu kuma da gangan suka ki bin umarnin wannan kotun bai share hukuncin ba har sai kotun ta janye wannan hukuncin na farkon"

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci