OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

KADIRS ta rufe wasu Otal da sauran wuraren kasuwanci saboda rashin biyan haraji

KADIRS ta rufe wasu Otal da sauran wuraren kasuwanci saboda

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kaduna, KADIRS, ta rufe wasu otal guda biyu, da wurin taro, da kuma wuraren kasuwanci daban-daban a cikin babban birnin Kaduna, saboda rashin biyan harajin da ya kai Naira miliyan 422.6.

Wadanda abin ya shafa sun hada da Seals Admiralty Naval Suites mallakar Navy Travels and Tours, Abuja Deluxe Suites dake kan titin Ali Akilu Kaduna, da sauran su kamar Big City Event Centre, Bijo Surgical & Scientific Limited, Zedvance Finance Limited, TXTLight Power Solution, Lek. 

Sakatariya kuma mai ba da shawara kan harkokin shari’a ta KADIRS Aysha Ahmad, ta bayyana cewa, an rufe guraren sana'ar ne domin tabbatar da yan kasuwa na biyan haraji hadi da bin ka’idojin.

Ta kuma jaddada cewa KADIRS ta yi aiki ne da sashe na 104 na dokar harajin inda ta rufe harabar "ba mu da wani zabi face ikon da doka ta ba mu. Wannan shine dalilin da ya sa muke tsare harabar,” in ji ta. 

Ta jaddada cewa KADIRS ba ta samu wani farin ciki ba wajen rufe kadarori ko wuraren kasuwanci na wadanda suka kasa biyan haraji, inda ta kara da cewa biyan haraji nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane dan kasa. 

Sakatariyar hukumar ta ce wannan na daga cikin matakan da suka dauka na cimma tattara kudaden shiga har Naira biliyan 120 da gwamnatin Kaduna ta gindaya don gudanar da ayyukanta.

Don haka ta yi kira ga al’ummar jihar da su tabbatar da biyan haraji a kan lokaci domin wani nauyi ne daya rataya a wuyan al’umma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci