OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Dan Majalisar Hon Isag Dogon yaro ya rasu

Dan Majalisar Hon Isag Dogon yaro ya rasu

House of Representatives

Majalisar Wakilai ta sanar da rasuwar Hon Isa Dogonyaro dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura/Garki ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10. 

 

Dan majalisar wakilan ya rasu ranar Juma'a bayan gajeriyar rashin lafiya kamar yadda wata sanarwa da kakakin majalisar wakilai Hon Akin Rotimi a Abuja ya fitar ya bayyana haka. 

 

Sanarwar tace “A cikin bakin ciki ne muka sanar da rasuwar Hon. Isa Dogonyaro (Kogunan Ringim), fitaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura/Garki ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10.b Allah ya yi wa Hon.Dogonyaro rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya.” 

 

“Hon. Isa Dogonyaro ya kasance dan majalisa mai kwazo da kishin kasa, wanda ya yi wa al’ummar mazabarsa da kasa hidima da jajircewa sosai, ya kasance ginshiki a majalisar, wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samar da dokoki, musamman a fannin yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da yaki da zazzabin cizon sauro. 

 

“An zabe shi a dandalin jam’iyyar APC Hon. Dogonyaro ya shahara da rikon amana da jajircewa da sadaukar domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya. Za a yi kewar sa sosai a zauren majalisar wakilai."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci