OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Obi Cubana ya bukaci gwamnati ta samar da kyaykyawan yanayin kasuwanci

Obi Cubana ya bukaci gwamnati ta samar da kyaykyawan yanayin

Shahararren dan kasuwa, Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana, ya jaddada bukatar gwamnatocin tarayya da na jihohi su ba da fifiko wajen samar da ingantaccen yanayi don bunkasa kasuwanci. 

 

A yayin wata hira da aka yi a wani taro da Gavice Logistics ta dauki nauyin shiryawa da ke mai da hankali kan fargado da kirkire-kirkire, wanda aka gudanar a ranar Asabar a Victoria Island, Legas.

 

 Iyiegbu ya jaddada muhimmancin sa hannun gwamnati wajen bunkasa ababen more rayuwa da inganta matakan tsaro don bunkasa harkokin kasuwanci.

 

Dan kasuwar ya bayyana cewa, samar da yanayin kasuwanci yana da matukar muhimmanci wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman matasa.

 

Ya ce, "Suna buƙatar hanyoyi masu kyau don jigilar kayansu ." Ya yi kira ga gwamnatoci da su gina tituna masu kyau da kuma samar da mafita mai dorewa kan rashin tsaro. 

"Matasa ba sa bukatar gwamnatoci su saya musu ababen hawa, sai dai a samar da yanayin da zai dace da kuma kawar da shingaye a kan hanyar. Mutane suna siya da siyarwa, amma yawan harajin da ake karba yayi yawa. Haka kuma, ya kamata mutane su rika zirga zirga daga wannan wuri zuwa wancan ba tare da fargabar an yi musu fashi ko sace su ba,” inji shi. 

 

Iyiegbu, wanda shi ne Shugaban kamafanonin Cubana, ya shawarci matasa da su kasance masu kirkire-kirkire kuma a shirye suke su yi aiki tare dasu domin samun nasara.

 

”Akwai lokutan da abubuwa ke da wahala da kuma lokutan da kasuwancin ke tafiya sosai. kuma tare da kowane ƙalubale da ake fuskanta, dole ne ku san yadda za ku tsalle shi kuma ku ci gaba da tafiya zuwa mataki na gaba har sai kun yi nasara.Don haka dole ne masu kasuwanci musamman matasa su kasance masu kirkire-kirkire,” inji shi

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci