OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan bindiga sun kai hari jami'ar CUSTEC dake Kogi

Yan bindiga sun kai hari jami'ar CUSTEC dake Kogi

A ranar Alhamis da daddare ne wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai wa jami’ar Confluence University of Science and Technology, CUSTEC, Osara, Okene a Jihar Kogi hari, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai. 

 

A cewar wani shaidar gani da ido, ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar da misalin karfe 9:00 na dare a yayin da daliban ke karantun jarabawa.

 

 Majiyar ta ci gaba da cewa ‘yan bindigan sun shigo ta cikin daji ne, suka shiga dakunan karatu uku suka fara harbin iska, inda majiyar ta ce: “Sun kama daliban dake dakin karatun, sun jefa makarantar ta cikin rudani, yayin da daliban suka fara guje-gujen neman tsira"

 

Daga bisani jami'an tsaron makarantar sun yo arangama da Yan bindigar inda sukayi nasarar dakatar dasu daga cigaba da dibar daliban suyi garkuwa da su.

 

 Kamar yadda rahotanni suka nuna, daliban na shirye-shiryen jarabawar semester ta farko da ake sa ran za a fara ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.

 

 Wani dalibi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce shi da wasu dalibai sun gudu zuwa daji suka boye a can na "fiye da awa daya" har saida komai ya lafa.

 

Shugaban jami'ar CUSTEC, Farfesa Abdulraman Asipita, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ki bayar da cikakken bayani kan adadin daliban da aka sace. "Ba na magana da 'yan jarida a kan irin wannan lamari, amma ina so ku sani cewa muna dukkan kokarin wajen shawo kan lamarin."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci