OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Garuruwa 225 Ne Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihohin Kano Da Jigawa - NEMA

Garuruwa 225 Ne Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihohin Kano Da Ji

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA), ta bayyana cewa garuruwa 225 na jihohin Kano da Jigawa ne ambaliyar ruwa ta shafa daga watan Yuli zuwa Agusta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kodinetan hukumar na yankin Kano da Jigawa, Nuradeen Abdullahi ya fitar yau (Asabar).

Abdullahi ya bayyana cewa a ranar 16 ga watan Agusta hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama sama da yadda aka saba a jihohi 19 da suka hada da Kano da Jigawa tsakanin watan Agusta da Satumba.

Kananan hukumomin da abin ya shafa a jihar Kano sun hada da Tudun Wada, Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono, Tsanyawa, Rimin Gado da Dawakin Kudu.

Haka kuma yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Jigawa sun hada da kananan hukumomin Kafin Hausa, Malam madori, Hadejia, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Kaugama, Babura, Gwaram, Dutse da Kirikasamma.

Yayin da yake lura da asarar kadarori da ababen more rayuwa da ambaliyar ruwa ta ja, Abdullahi ya kara da cewa: “Ina kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wurin Kara shiri akan abin da ka iya bullowa,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Ko’odinetan ya kuma gargadi mazauna yankin kan toshe magudanun ruwa tare da shawartan su da su rika bin sakonnin gargadi.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin da su fara gangamin wayar da kan jama’a a jihohin su domin dakile faruwar lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci