OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

EFCC Ta Kama Wani Da Katin ATM 576 a Filin Jirgin Saman Kano

EFCC Ta Kama Wani Da Katin ATM 576 a Filin Jirgin Saman Kano

Hukumar Yaki da cin hanci EFCC ta kama wani dake hanyar sa na zuwa Uganda, Khalil Bashir Lawal da katin ATM 576 a filin jirgin saman Kano.

An kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Aminu Kano da ke Jihar Kano kwanaki kadan bayan da EFCC ta kama wasu mutane uku da katin ATM 1,144.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya ce an kama mutanen ne a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa, aikin da ya kai ga cafke wanda ake zargin yana tare da hadin gwiwar jami’an tsaron jiragen sama da kuma hukumar kwastam ta Najeriya.

An samu wanda ake zargin da katin ATM guda 576 da sunaye daban-daban da kuma bankuna a boye a cikin jakarsa kafin a kama shi.

Uwujaren ya kara da cewa za a gurfanar da Khalil a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Jamilu Shehu ta samu wasu mutane uku da aka kama a filin jirgin saman na Aminu Kano da katin ATM guda 1,144 da laifi.

An yanke wa wadanda ake zargin hukuncin zaman gidan yari na watanni shida a ranar Litinin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci