OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Masari ya dage dokar hana zirgazirgar babura da daddare a Katsina

Masari ya dage dokar hana zirgazirgar babura da daddare a Ka

Katsina Governor, Aminu Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya dage dokar hana zirgazirgar babura da daddare a fadin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Al-Amin Isah ya fitar.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, sanarwar ta kara da cewa: “A bisa la’akari da bikin maulidi Gwamna Masari ya amince da dakatar da dokar hana zirgazirgar babura da daddare.

“Dakatarwan zai ƙare ne a ranar 20 ga watan Nuwamba. 

"An umurci jama’a da su kasance masu bin doka yayin dakatar da zirgazirgan.

“An kuma shawarci jama’a da su yi taka tsantsan tare da taimaka wa jami’an tsaro wajen inganta zaman lafiya da tsaro a jihar."

Ku tuna cewa gwamna Masari ya sanya dokar ne a lokacin da ayyukan ‘yan bindiga ke ruruwa a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci