OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dakarun Sojoji Dake Sintiri Sun Kashe ‘Dan Bindiga, Sun Kama Guda Uku a Kaduna

Dakarun Sojoji Dake Sintiri Sun Kashe ‘Dan Bindiga, Sun Ka

Rundunar sojin sintiri karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta daya ta Najeriya (1 Div.), Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ta yi nasarar kashe dan bindiga guda tare da kama wasu uku a jihar Kaduna.

Rundunar sojin sintirin da ta kunshi kwamandojin yaki sun fatattaki ‘yan bindigan a garuruwan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da Dogon Dawa na jihar.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu ne ya bayyana hakan a yau ( Talata).

Nwachukwu ya ce sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigan ne a jiya wanda ya kai ga kama mutane uku tare da kawar da daya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A fadan da aka yi tsakanin ‘yan bindigan, jami’an sojin sintiri sun ci galaba a kan ‘yan bindigan da karfi, tare da kashe daya daga cikin su, yayin da aka kama wasu uku da ransu, yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka tsere da raunukan harbin bindiga. "

Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan bindigan sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya, harsashi na musamman 7.62 mm guda 27 da kuma babura 18.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma musamman cibiyoyin kiwon lafiya da ma’aikatan lafiya da su kula da mutanen da za su iya neman magani sakamakon raunukan harbin bindiga, sannan su kai rahoto ga hukumomin tsaro da abin ya shafa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci