OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

DA DUMI-DUMI: 'Yan Bindiga Sun Sace Basaraken Gargajiya Imo

DA DUMI-DUMI: 'Yan Bindiga Sun Sace Basaraken Gargajiya Imo

A safiyar Alhamis ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da wani basarake mai suna Eze Damian Nwaigwe a masarautar Mbutu dake jihar Imo.

‘Yan bindigan wadanda sun kai kimanin mutanen 10, sun isa fadar ne da misalin karfe 2:30 na safe suna harbe-harbe.

A cewar wani wanda ya bukaci a sakaye sunan sa, basaraken ya gina fadarsa ne a wani waje mai nisa da mutane, wanda hakan ya sa aka kai masa hari cikin sauki.

Mazauna kauyen sun bayyana damuwar su game da tsaron lafiyarsu tunda har za'a iya sace shugaban su.

Wani ganau yace bayan harbe-harben da 'yan bindigan suka yi jama'a sun kasa komawa bacci saboda firgici.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Micheal Abattam ne ya tabbatar da lamarin. 

A cewar sa, ‘yan sanda sun fara farautar ‘yan bindigar da suka tsere tare da yin garkuwa da basaraken. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci