OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Da Osinbajo Zasu Kashe Naira Biliyan 11 Akan Abinci Da Tafiye Tafiye

Buhari Da Osinbajo Zasu Kashe Naira Biliyan 11 Akan Abinci D

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo za su kashe Naira biliyan 11.92 wajen tafiye-tafiye da kuma abinci.

Adadin da aka ambata ya kuma haɗa da Naira biliyan 1.58 da aka ware domin gyaran jiragen sama.

A hannu guda kuma ƴan majalisar dokokin ƙasar za su samu naira biliyan 100 domin gudanar da ayyukan mazabu.

Yayin da a cewar hukumar yaƙi da cin hanci rashawa da sauran laifuka masu alaƙa suka bayyana hakan a matsayin saɓawa doka..

A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaba Buhari ya gabatar da ƙudirin kasafin kudin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 20.51 ga taron hadin gwiwa na majalisar dokokin ƙasar.

Kasafin kuɗin ya kai kusan Naira biliyan 750 sama da Naira Tiriliyan 19.76 da aka gabatar a baya.

Gwamnati za ta kashe Naira miliyan 250 wajen samar da mai na jiragen sama yayin da sayan kayan zirga-zirgar jiragen sama da na tsaro zai dauki Naira biliyan 1.50.

Sa'annan Naira miliyan 650 za'ayi amfani dasu wajen gina sabon filin saukar jirage masu saukar ungulu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci