OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnan Kwara yakai ziyarar taya murna makaranta mafi yawan daliban da sukayi nasara a JAMB

Gwamnan Kwara yakai ziyarar taya murna makaranta mafi yawan

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyarar taya murna makarantar Eucharistic Heart of Jesus College dake Ilorin domin yabawa da gwazon daliban da suka samu maki tsakanin 300 zuwa 355 a jarrabawar samun gurbin karatu a jami'a da aka yi kwanan nan, UTME. 

 

Gwamnan ya ce ziyarar da ya kai makarantar wata alama ce ta nuna gamsuwa da kokarin daukacin daliban Kwara a fadin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da suka zo na daya a jarabawar. 

 

“Ina nan a yau a madadin jama’a da gwamnatin jihar Kwara in ce muna alfahari da ku da sauran irin ku a fadin jiharmu. Muna alfahari da nasarorin da wannan makaranta ta samu domin ku kadai kuna da dalibai 35 da suka ci sama da 300 a UTME. Don haka na kawo ziyara don in taya ku murna tare da ba ku kwarin gwiwa kan kara himma,” in ji AbdulRazaq.

 

 Ya kuma bukaci daliban da ke kananan azuzuwa da su kara himma tare da zarce sakamakon bana a shekaru masu zuwa “Ga wadanda ke kananan aji, a nan da kuma fadin jihar mu, ina son in ba ku kwarin guiwa a shekara mai zuwa. Ina taya shugaban makarantar da sauran ma’aikata murna bisa wannan aiki da aka yi.

 

 “Ina kuma karfafawa shugaban makarantar da ma’aikata gwiwa da su tallafawa sauran makarantun jihar da sirrin nasarar su"in ji gwamnan.

 

 Shugabar kwalejin, Rev. Sister Margaret Ihinolurinjan, ta bayyana mamakin wannan ziyarar tare da gode wa gwamna AbdulRazaq bisa wannan karramawa da kwarin gwiwa daya basu.

 

"muna yin iyakacin kokarinmu mu cusawa dalibanmu tarbiyya. Ba ma wasa da horonmu da koyo da koyarwar da muke ba su. Ba ma wasa da tsarin karatun mu."

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci