OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

"Muna da sama da lita biliyan daya na man fetur a ajjiye"-NNPCL

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya gargadi masu ababen hawa da su guji shiga firgici da siyan man fetur suna boyewa domin kamfanin yana da isasshen mai a ajjiye.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban jami’in yada labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, a ranar Talata. 

A cewar sanarwar, kamfanin ya jaddada cewa an samu ci gaba sosai a fannin samar da man fetur da kuma rarraba man fetur a fadin kasar nan.

Sanarwar ta ce, “Kamfanin yana so ya bayyana cewa a halin yanzu yana da sama da lita biliyan 1.5 na man fetur wanda shine kwatankwacin wadatar kwanaki sama da 30.

“Haka zalika, NNPC Ltd. na hada kai da hukumomin da abin ya shafa, irin su Niger Midstream & Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), kungiyoyin kwadago a fannin da jami’an tsaro, domin magance matsalar sace-sacen man fetur da sauran ayyukan da ba su dace ba.”

Jami’an NNPC sun gudanar da cikakken bincike inda suka sanya ido kan gidajen mai a jihohi daban-daban, ciki har da Legas da babban birnin tarayya, FCT inda layukan man fetur din sun ragu matuka.”

Sanarwar ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa, wannan kyakkyawan yanayi zai ci gaba da yaduwa zuwa wasu jihohi nan da kwanaki masu zuwa. 

Sanarwar ta kuma jaddada aniyar kamfanin na NNPC na tabbatar da samar da mai a fadin kasar nan tare da dakile duk wata matsala da ka iya kawo cikas a harkar rarraba mai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci