OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Uwargidan shugaban kasa ta karrama soja mace ta farko data kammala wani horo na musamman a burtaniya

Uwargidan shugaban kasa ta karrama soja mace ta farko data k

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, a ranar Litinin din da ta gabata ta karbi bakuncin ‘yar Najeriya mace ta farko da ta kammala karatu a Royal Military Academy Sandhurst da ke kasar Burtaniya, Laftanar Oluchukwu Owowoh ta biyu.

 

 A watan Afrilu, mai shekaru 24, Owowoh tare da sauran jami'an Cadets 134 a Landan sun gudanar da faretin Sovereign's Parade, wanda ke nuna ƙarshen makonni 44 na horo kan dabarun aikin soja.

 

 A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Kukoyi Busola, Uwargidan shugaba kasar tace ta yabawa Owowoh bisa bajintar da ta yi da jajircewar da ta yi a lokacin horon. inda ya bayyana ta a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya. 

 

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa, “jajircewarki abu ne mai matukar ban mamaki, kuma kin zaburar da matasan kasar nan, a matsayinki na mace, wadda ta fara taka rawar gani a fagen da maza suka mamaye, ina jinjina miki.

 

 "Yanzu kin zama abin koyi ga daukacin matasan Najeriya, idan kin ci gaba da mai da hankali za ki cimma dukkan burin ki a rayuwa."

 

Sanarwar ta kuma ce uwargidan shugaban kasar ta bukaci halartar matar mataimakin shugaban kasa, uwargidan shugaban majalisar, matan ministoci, matan hafsoshin sojan Najeriya su jinjinawa 2nd Laftanar Owowoh.

 

 Sanarwar ta kara da cewa, kwamandan makarantar horas da sojoji ta Najeriya, Manjo Janar OJ Ochai, ya bayyana cewa, “Owowoh ta kasance mafi jajircewa a cikin zababbun daliban jami’ar NDA guda 200.” 

 

Sanarwar ta kara da cewa, "Tuni an turata aikin da sashin leken asiri na sojojin Najeriya bayan dawowarta kasar daga burtaniya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci