OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar gwajin lafiya kafin aure

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar gwajin la

Kano Governor, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan dokar gwajin lafiya kafin aure a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sunusi Bature Dawakin Tofa, Daraktan yada labarai na gwamnatin a ranar Talata.

Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da takardar shaidar tantance lafiyar ma' auratan. Dokar ta tilasta gwajin ciwon hanta wato hepatitis B da C, HIV/AIDS, da gwajin jini domino gano cutar sikila da sauran cututtuka masu alaka da su kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Dokar ta zama wajibi don rage yiyuwar haihuwar yara da wasu matsalolin kiwon lafiya kamar su sickle cell anemia, HIV/AIDS, da kuma ciwon hanta.

Sanarwar tace “Dokar ta wajabta yin gwajin cutar kanjamau, Hepatitis, genotype, da sauran gwaje-gwajen da suka dace kafin aure. Har ila yau, ta haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen da ke dauke da cutar kanjamau, sickle cell anemia, hepatitis. 

A yayin da yake rattaba hannun, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce kuma tabbatar da haihuwar ‘ya’ya masu lafiya.

Bayan amincewar majalisar dokokin jihar an sanya hannu kan dokar a ranar 6 ga Mayu 2024 kuma za ta fara aiki daga ranar 13 ga Mayu, 2024. 

Sanarwar ta kara da cewa, "Dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin saba wa tanadin ta, ya aikata laifi, kuma idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar tarar Naira dubu dari biyar, ko zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar, ko kuma duka biyun."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci