OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bauchi Da Jihohi Biyar Za Su Sha Ruwan Sama Na Kwana Hudu - NiMet

Bauchi Da Jihohi Biyar Za Su Sha Ruwan Sama Na Kwana Hudu -

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya na kwanaki hudu a jihar Bauchi tare da wasu jihohi biyar na Arewa.

Hukumar a wani kiyasi da ta fitar, ta bayyana cewa ruwan saman zai shafi babban birnin tarayya Abuja, jihohin Kaduna, Neja, Filato da Nasarawa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jihar Gombe da wasu su yi tsammanin ruwan sama mai matsakaicin karfi a lokacin da aka ambata. 

Sauran jihohin yadda rahoton ya bayyana sun hada da: “Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Akwa Ibom, Jihohin Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Rivers, Edo da Delta.”

Rahoton ya ci gaba da cewa: “Ana sa ran samun ruwan sama kadan ko kuma babu wasu jihohi kadan.

"Sakamakon ruwan sama mai karfi da ake sa ran a wasu sassan tsakiyar biranen kasar da kuma karancin ruwan sama da ake sa ran za a samu a yankin kudu maso gabashin kasar na tsawon kwanaki biyu a jere, akwai yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a kan tituna, da kananan matsuguni da magudanan ruwa," hukumar ta sanar.

Hukumar ta kuma ce yayin da ake sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaici da kuma mai karfin gaske a jihohin arewa da tsakiyar kasar, ya kamata kuma a yi tsammanin iska mai karfi cikin wannan lokacin.

NiMet ta kuma gargadi jama'a da su nisanci tuki ta hanyar da ruwan ke malala da kuma guje wa tsayawa a karkashin bishiya yayin ruwan. 

Hukumar ta kara da cewa a kashe na’urorin lantarki a lokacin da ake ruwa. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci