OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bauchi: Ambaliyar Ruwa Ta kashe Mutum Uku Da Lalata Gidaje Sama Da 1,000

Bauchi: Ambaliyar Ruwa Ta kashe Mutum Uku Da Lalata Gidaje S

Babban Darakta Janar na Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA), Ibrahim Kabir ya tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon ambaliyar ruwa a jihar.

Ya kara da cewa ambaliyar ta kuma lalata gidaje 1,453 da filayen noma a kananan hukumomin Zaki da Gamawa na jihar.

Kabir ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake zantawa da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ziyarar da ya kai domin jajanta wa al’ummar da abin ya shafa.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Kabir ya ce ambaliyar ta katse hanyoyin da suka hada kananan hukumomin biyu da wasu sassan jihar a wurare shida a kan babbar hanyar.

A cewar sa: "A matsayin matakin taimako, al'ummomin suna buƙatar kwale-kwale 14 a matsayin hanyar sufuri don ketare hanyoyin da suka yanke don ci gaba da kasuwancin su na yau da kullum."

Haka kuma, gwamnan ya jajanta wa al’ummomin kan barnar da ambaliyar ta yi da kuma asarar rayuka.

Ya kuma ba wa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) umarnin sayo kwale-kwale guda 14 da kuma daukar bayanan irin asarar da aka yi, inda ya ce hakan zai baiwa gwamnati damar daukar mataki na gaba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci