OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Atiku Ga Wike: Ba Zan Iya Tilasta Ayu Yayi Murabus Ba

Atiku Ga Wike: Ba Zan Iya Tilasta Ayu Yayi Murabus Ba

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce ba za a tilastawa Sanata Iyioricha Ayu murabus daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar PDP na kasa ba.

Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan matakin da gwamnan jihar, Nyesom Wike na jihar Ribas ya ɗauka na ficewa daga kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

A cikin sanarwar, Atiku ya ce: "Da sanyin safiyar yau hankalina ya karkata ga wani labari inda da dama daga cikin jiga-jigan jam’iyyarmu ta PDP suka yi jawabi ga manema labarai tare da bayyana cewa zasu fice daga kwamitin yaƙin neman zaɓe. 

"Da kuma jaddada ƙiran da suka yi a baya na yin murabus ko tsige shugaban jam’iyyar mu ta kasa Sanata Dr. Iyorchia Ayu a daya bangaren.

"Mutanen da suka yi magana da manema labarai dole ne su sami dalilansu na ficewa daga kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa, kuma ba zan yi hasashen ko mene ne wadannan dalilan ba.

"Ni kaina na yi matukar mamakin wannan janyewar, domin kamar yadda jami’an jam’iyyar mu suka shaida min, baya ga jam’iyyar PDP reshen Jihar Ribas, sauran jahohin tarayya da suka rage sun miƙa sunayen mutanen da suke so a shigar da su da kansu.

"Dangane da ƙiraye-ƙirayen murabus ko tsige shugabanmu na kasa, dole ne in sake maimaita abin da na fada a fili da kuma a boye; zan bayyana cewa, a matsayina na mai kishin dimokaradiyya kuma mai tsayin daka wajen bin doka da oda, tsari da bin doka da kundin tsarin mulkinmu, imanina ne cewa duk wani abu da za mu yi a jam’iyyarmu, dole ne a yi shi bisa ga doka da tsarin mulkinmu.

'Idan za a tsige Dr. Ayu daga mukamin, dole ne a yi shi bisa ga dokokin da suka gindaya ginshikin tsige, ruwaitowar Jaridar Vanguard.

"A kowane hali, za ku tuna cewa hukumar da doka ta ba da ikon fara wannan tsige wa daga mukaman, tuni ta amince da shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci