OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Jam'iyar Labour ta Caccaki Gwamnati Kan Lasisin Da Aka Bawa CONUA

ASUU: Jam'iyar Labour ta Caccaki Gwamnati Kan Lasisin Da Aka

Jam’iyyar Labour ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban Buhari ta ɗauka na amincewa da rijistar kishishar ASUU.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Sakataren Yaɗa Labarai na jam'yar na ƙasa, Comrade Arabambi Oluwafemi a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba.

Ya ce matakin da Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya jagoranta, "gurguwan shawara ce ne da ba za ta kawo wa harkar ilimi ɗa mai ido ba."

Mista Arabambi ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta samo hanyoyin kawo maslaha don mayar da dalibai makaranta maimakon haifar da rikici.

“Abin baƙin ciki ne a lura cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a Najeriya a yanzu su ne suka sa ilimi ya gagara ga talaka.

“A yayin da take nuna juyayi ga daliɓan da iyaye, jam’iyyar Labour tana yin ƙira ga ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU da gwamnatin tarayya da su haɗa kai da su samar da hanyar da ta dace don magance rikicin da ya dabaibaye su.”

A cewar jam'iyar, yanda gwamnatin APC ke mulki suna buɗa musu hanyane har zuwa lokacin da za su kore su daga gwamnati da bawa Peter Obi/Datti dama.

"Ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi yana da abin da ake bukata don mulkin ƙasar tare da kyakkyawan sakamako da tsarin mutuntaka."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci