OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA Ta Kama Hakimi a Sokoto Da Wasu Kan Safarar Kwayoyi

Hukumar NDLEA Ta Kama Hakimi a Sokoto Da Wasu Kan Safarar Kw

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta kama Hakimin kauyen Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sakkwato, Abubakar Ibrahim da wasu mutane goma sha daya da muggan kwayoyi.

Jami'an sun kama shine tare da wasu mutane sha daya inda aka yi nasarar kama kwayoyi tabar wiwi kilo 1,251, da kuma hodar iblis, a samamen da akayi a jihohi bakwai.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ta hannun mai magana da yawun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin Femi Babafemi.

Sanarwar tace jami’an tsaro sun kama muggan kwayoyi 225,000 a wani samame da suka yi a yankin Oshodi da ke jihar Legas a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba, cewar Jaridar Punch.

Sa'anna shima hakimin kauyen Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Abubakar Ibrahim, mai shekaru 38,  an kama shi a garin Bodinga a wannan rana tare da kilo 3 na miyagun kwayoyi.

A babban birnin tarayya Abuja, jami’an da suke sintiri a kan hanyar Kwali zuwa Abuja a ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, sun tare wata babbar mota dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 915.8 tare da kama wasu mutane uku: Kabiru Ibrahim, mai shekaru 40;  Muhammad Mu'awiyya mai shekaru 30 da Adamu Adamu mai shekaru 24.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A jihar Adamawa jami’an tsaro sun kama wasu masu safarar kan iyaka guda biyu, Abdullahi Mamuda (aka Mama) da Aliyu Abdullahi (aka Garga) a otal din Skylight da ke Jambutu a Yola ta Arewa.  

"A binciken da aka yi wa motar su, wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka an gano Tramadol 225mg guda 39, 320 a boye a sassa daban-daban na kofar motar.

Ya kara da cewa, a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas, jami’an NDLEA da ke dangatakar shigo da kaya ta SAHCO a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, sun kama kwali 15 dauke da kwayoyin Tramadol 802,000 da aka shigo da su daga Dubai, UAE da Karachi, Pakistan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci