OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ɗan Majalisar Katsina Ya Rasu A Ƙasar Saudiyya

Ɗan Majalisar Katsina Ya Rasu A Ƙasar Saudiyya

Photo Source: Legit Hausa

Wani Mamba mai wakiltar karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina ya rasu a ƙasar Saudiyya.

Ɗan majalisar mai suna Dakta Ibrahim Aminu Kurami dai yaje ƙasar ta Saudiyya ne domin yin aikin hajji ƙarama wato Umrah.

A cewar Jaridar Daily Trust, ɗan majalisar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya da ya yi a Madina.

Rahoton yace Dr. Aminu ya rasu ne da misalin karfe biyu na safe agogon Najeriya.

Yayin da marigayin yabar mata biyu da ƴaƴa 11 da jikoki uku.

Ɗan majalisar dai mai rasuwa an zaɓe shi ne a matsayin ɗan majalisar dokokin jihar Katsina a zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar 31 ga watan Oktoba, 2020.

Marigayin ya maye gurbin  
Hon. Abdurrazak Ismail Tsiga wanda shima ya rasu akan mulki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci