OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ɗan Ƙasar China Da Ake Zargi Da Kisan Budurwar Sa A Kano Ya Musanta Aikata Laifin

Ɗan Ƙasar China Da Ake Zargi Da Kisan Budurwar Sa A Kano Y

Geng Quarong, ɗan ƙasar China da ake zargi da kashe budurwarsa mai shekaru 23, UmmuKulsum Sani a Kano,  ya musanta aikata laifin.

A ranar Alhamis ne dai aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban babbar kotun jihar Kano.

An gurfanar da shi ne a ƙarƙashin sashe na 221 na dokokin penal code, da hukuncin kisa.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta abin da kotu take tuhumarsa akai.

A dalilin haka mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16,17 da 18 ga watan Nuwamba domin sauraren ƙarar.

Sa'annan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali.

Wasu ƴan kungiyar Jan Bulo da ke Kano ne suka daƙile Quanrong bayan ganin shi a ɗakin marigayiyar ɗauke da wuƙa da jini kimanin wata ɗaya da ya wuce.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci