OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin yiwa yara rigakafin shan inna

Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin yiwa yara rigakafin sha

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na fara aikin allurar rigakafin cutar shan inna na kwanaki hudu da za'ayiwa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a fadin jihar.

 

Jami’in wayar da kan al'umma a hukumar kula da lafiya matakin farko Rabi’u Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayin wani taron da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar hukumar suka shirya a jiya Alhamis. 

 

A cewarsa, za a fara rigakafin a ranar 20 ga watan Afrilu har zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2024.

 

 "Ma'aikatan mu zasu bi gida-gida, da makarantun boko dana islamiyya don yiwa yara yan kasa da shekaru biyar allurar rigakafin cutar shan inna"

 

 “Har ila yau, tawagarmu za ta bi lungu da sako harma da kan tituna da kasuwanni domin tabbatar da anyiwa yara da dama allurar rigakafin,” a cewar sa.

 

Ibrahim ya kara da cewa, a wannan karon jami'an hukumar zasu je makarantu daban-daban da suka hada da na gwamnati, masu zaman kansu, dana Islama.

 

 "Manufar ita ce samar da al'ummar da ba ta da cutar shan inna," in ji Ibrahim.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci