OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

APC tayi watsi da hukuncin kotun daya dakatar da Ganduje

APC tayi watsi da hukuncin kotun daya dakatar da Ganduje

APC National Chairman, Abdullahi Umar Ganduje

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC yayi watsi da umarnin kotu na dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, Inda tace hakan ya saba da doka. 

 

A ranar Laraba ne wata babbar kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga shugabancin jamiyyar inda ta kuma haramta masa bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar APC.

 

 Matakin dai ya biyo bayan karar da Haladu Gwanjo da Laminu Sani suka shigar, suna kalubalantar take hukuncin da suka yanke na dakatar da Ganduje a mazabar sa da kwamitin zartarwar jamiyyar a matakin jiha yayi.

 

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja a ranar Larabar nan mai baiwa jamiyyar shawara kan harkokin shari’a a matakin jiha na jam’iyyar, Farfesa Abdulkarim Kana ya dage cewa hukuncin kotun ba shi da tushe. 

 

Taron manema labarai ya biyo bayan ziyarar ban girma da shugabannin jamiyyar a mazabar Ganduje suka kaiwa shugaban jamiyyar na kasa.

 

Farfesa Abdulkarim ya jaddada wadanda suka shigar da karar ba halastattun yan jamiyyar APC bane.

 

"a yammacin yau muke jin labarin hukuncin kotu Kuma munsan takardar da akayi amfani da ita wajen shigar da karar akwai zamba a cikin lamarin saboda haka duk wani hukunci da aka yanke sanadiyar irin wannan takarda to doka bata aminta dashi ba" a cewar sa.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci