OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Tarayya zata maida mafi karancin shekarun shiga jami'a shekara 18

Gwamnatin Tarayya zata maida mafi karancin shekarun shiga ja

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar kara mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu zuwa shekaru 18.

 

Ministan Ilimi, Tahir Mamman, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake sa ido a kan jarrabawar share faggen shiga jami'a a Abuja, ya gargadi iyaye da su guji takurawa ’ya’yansu akan karatu ya wuce kima.

 

Mamman ya ce “Wani abin da muke sake yin duba a kansa shi ne karancin shekarun wadanda suka nemi gurbin karatu a jami’a. Wasu daga cikinsu sun yi kankanta da yawa su fahimci menene ilimin jami'a."

 

 "Wannan shine matakin da ɗalibai ke barin gaban iyayensu su fara cin kashin kansu, to idan sunyi kankanta za'a samu matsala kamata yayi ace dalibai sai sun kai shekaru 18 kafin su Shiga amman samun kananan yara a jami'a ne yasanya muke samun matsalolin da muke gani a jami’o’i a yanzu. Yakamata a ja kunnen iyaye da kada su matsawa ‘ya’yansu su kammala makarantar sakandire da wuri"

 

Ya yabawa hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB bisa yadda ake gudanar da jarabawar tare da lura da yadda ake amfani da fasahar zamani.

 

 Mamman ya ce “Matsalar satar jarrabawa ta Ragu matuka zuwa kashi 100 daga cikin miliyan 1.2 sanadiyar amfani da fasahar zamani don haka yana da kyau kwarai.” 

 

A nasa bangaren Karamin Ministan Ilimi Tanko Sununu, wanda ya bayyana jin dadinsa da cewa ana ci gaba da gudanar da jarabawar UTME a Saudiyya.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci