OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 10, ta Lalata Gidaje Da Gonaki a Bauchi

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 10, ta Lalata Gidaje Da Gonaki

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a cikin jihar.

Sakamakon ambaliyar ruwan, gidaje da gonaki da dama sun lalace tare da yin sanadin mutuwar mutane goma.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba a wata hira da aka yi da shi, Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar, Adams Nayola ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa ambaliyar ta tilastawa mutane barin gidajen su.

A cewar sa: “Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukan su yayin da hekta daya na gonaki da gidaje suka lalace a wasu sassan jihar.

“Kananan hukumomin da abin ya fi shafa sun hada da Jama’are, Giade, Misau, Dambam, Zaki, Darazo, Kirfi, Itas-Gadau, Shira, Gamawa da Toro.

"Duk da cewa ambaliyar ta shafi kananan hukumomi 19 cikin 20 na jihar Bauchi, kananan hukumomi goma sha biyu ne kawai suka fi fuskantar matsalar."

Ya kara da cewa tuni hukumar ta fara shirye-shiryen wayar da kan jama’a inda ta yi kira ga mutanen da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa da su kaura.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci