OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

A Karo Na Biyu Wike, Makinde Da Ortom Sun Sake Barin Ƙasar

A Karo Na Biyu Wike, Makinde Da Ortom Sun Sake Barin Ƙasar

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da takwarorin sa na Oyo, Abia da Benue sun tafi ƙasar Spain.

Hakan na zuwa yayin da rikicin jam'iyar PDP ke ƙara ta'azzara bayan ƙiraye-ƙirayen da Gwamna Wike yake na cewa sai Shugaban J'iyar yayi murabus.

Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da babban zaɓen da ke tafe na shekarar 2023.

A Daren Juma'a bayan hirar sa da kafafen yaɗa labarai a Fatakwal kan saɓanin sa da shugaban Jam'iyar PDP Sanata Iyorcha Ayu Gwamnan ya bar ƙasar.

Rahoton yace anga Gwamna Wike tare da Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia, da Samuel Ortom Benue a filin jirgin sama na Port Harcourt.

Yayin da Wike da sauran abokan tafiyar sa suka tashi da sanyin safiyar Asabar a Omagwa a karamar hukumar Ikwerre.

Wani jigon jam’iyyar ya tabbatar da hakan “Eh, gaskiya ne, Sun tafi Spain da sanyin safiyar Asabar, amma ba zan iya cewa ga dalilin tafiyar ba."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci