OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Addu’o’in Ku Muke Bukata, Ba Gargadin Ta’addanci Ba – Martanin Ministan Tsaro Ga Kasar Amurka

Addu’o’in Ku Muke Bukata, Ba Gargadin Ta’addanci Ba �

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce Najeriya na bukatar addu’o’i daga gwamnatin Amurka, ba wai gargadin ta’addanci da zai tashi hankulan‘yan Najeriya ba.

 

Mista Magashi ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake amsa tambayoyi daga mambobin kwamitin tsaro na majalisar wakilai a yayin zaman majalisar.

 

Ya bayyana cewa an tattauna sanarwar hari da gwamnatin Amurka ta fitar a taron kwamitin tsaro na ranar Litinin.

 

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne ma’aikatan Amurka da Birtaniya a Najeriya suka fitar da sanarwar tsar kan hare-haren ta’addanci a Abuja.

 

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka a ci gaba da fuskantar barazanar ta amince dauke 'yan kasarta da ke son barin Najeriya saboda harin ta'addanci.

 

Ofishin jakadanci na kasar Amurka ya kuma dakatar da ayyuka a ofishin da ke Abuja.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci