OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: An Gano Sunan Sanatan PDP Chimaroke Nnamani A Ƴan Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu

2023: An Gano Sunan Sanatan PDP Chimaroke Nnamani A Ƴan Kwa

An gano sunan ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas a majalisar dattawa, Sanata Chimaroke Nnamani, a matsayin mamba na kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan na zuwa ne yayin da kwanaki kadan ya rage a fara yakin neman zaben shekarar 2023 a hukumance.

Cikin jerin sunayen da APC ta fitar ranar Juma’a, ya kunshi mambobi 422.

Rahotanni  na cewa Sanata Chimaroke, wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, an saka shi a matsayin memba Daraktoci da Sakatarorin Daraktoci a cikin jerin sunayen kansilolin.

Idan za'a iya tunawa, dan majalisar ya wallafa wasu sakonni a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana Tinubu a matsayin “ ɗan siyasar da ya fi kowa aiki tukuru a wannan zamani”.

Tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da  zargin tsohon gwamnan Legas na rashin lafiyarsa, yana mai cewa masu yi wa Asiwaju ba'a ma suna iya samun nasu kason daga baya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci