OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: An Cire Sunan Aregbesola, Nnamani Daga Tawagar Yakin Neman Zaben Tinubu

2023: An Cire Sunan Aregbesola, Nnamani Daga Tawagar Yakin N

An cire sunan tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola daga cikin tawagar yakin neman zabe na jam'iyyar APC mai mulki.

 

Haka zalika sunayen da aka cire sun hada da tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, da na jihar Abia, Orji Uzor Kalu, da kuma Kassim Afegbua, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Edo.

 

An cire sunayensu ne a cikin sabon sunaye da sakataren jamiyyar APC na kasa, Iyiola Omisore ya fitar a yammacin Laraba.

 

Sunayen da aka fitar na farko wanda James Faleke ya fitar a watan Satumba, akwai sunayensu a matsayin mambobin majalisar a sassa daban-daban.

 

An kafa majalisar ne domin hada kan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC, Bola Tinubu, na zabe mai gabatowa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci