OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zamfara: Ƴan Bindiga Sunyi Barazanar Mayar Da Wanda Sukayi Garkuwa Dasu Ƴan Ta'adda

Zamfara: Ƴan Bindiga Sunyi Barazanar Mayar Da Wanda Sukayi

Ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da ƴaƴa mata biyu na tsohon Akanta Janar na Jihar Zamfara, Abubakar Bala Furfuri sun yi barazanar mayar da su ƴan ta’adda.

Ƴan ta'addan sun ce matakin zai tabbata idan Furfuri bai biya kuɗin fansa ba.

Ƴan ta’addan sun bayyana barazanar nasu ne a wani faifan bidiyo da aka fitar ranar Litinin.

Ƴan matan da aka sace dai sun shafe kwanaki 128 a hannunsu tun watan Yuni.

Rahoton Allnews ta ruwaito cewa an ga matan uku riƙe da bindigogin kakkaɓo jiragen sama a cikin bidiyon.

An ji wani ɗan ta’adda a bayan fage yana cewa: “Ba damuwan mu kudin bane, Za mu yi amfani da ku kawai mu ƙara yawan mayaƙa ko kuma amfani da ku yayin sabbin hare-haren mu."

A cikin wani roƙo na tausayawa a cikin bidiyon, ɗaya daga cikin ƴaƴan mai suna Zulaihat ta ce: “Sunana Zulaihat ƴar Zamfara.

“Don Allah baba, idan ka ga wannan bidiyon ka taimaka ka cece mu daga wannan halin. 

"Muna cikin mawuyacin hali muna zaune a nan, Ku yi watsi da masu ba ku shawara game da biyan kuɗin fansa.

"Don Allah, kada kar bar mu mu ƙara wata rana a cikin wannan yanayin.

“Sun yi barazanar cewa za su ba mu wani abu da zai sa mu manta da kai kuma ba za ka ƙara ganin mu ba.

"Sun ce za mu nuna musu gidajen attajirai kuma za mu tafi makarantu da su don sace yara, Don Allah a taimaka ka cece mu daga wannan halin," in ji ta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci