OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Zaben Fidda Gwani: Wakilin APC Daga Jigawa Ya Rasu A Abuja

Zaben Fidda Gwani: Wakilin APC Daga Jigawa Ya Rasu A Abuja

Wakilin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar Jigawa mai suna Alhaji Isa Baba Buji ya rasu.

Wakilin ya rasu ne a ranar Talata a Abuja yayin da ake ci gaba da gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar.

Buji ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar APC ta kudu maso yammacin jihar kafin rasuwarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya mutu ne da safe a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa a lokacin da yake shirin halartar babban taron jam’iyyar.

Kakakin jam’iyyar APC na jihar Jigawa, Bashir Kundu ya tabbatar da hakan.

Kundu ya ce, “Ya fadi a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti ya rasu kafin ya isa asibitin. Da muka isa asibitin an tabbatar da rasuwarsa,” kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci