OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Katsina ta gargadi maniyata su guji safarar miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki

Gwamnatin Katsina ta gargadi maniyata su guji safarar miyagu

Gwamnatin jihar Katsina ta gargadi maniyyatan da ke shirin gudanar da aikin Hajjin bana na 2024 kan safarar miyagun kwayoyi da wasu haramtattun kayayyaki zuwa kasa mai tsarki.

 

 Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Yunusa Abdullahi Dankama ya bayyana haka a ranar Alhamis a Katsina. 

 

Dankama ya ce hukumar ta yi wa maniyyata 2,600 rajista a jihar domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024, inda ya kara da cewa gwamnan jihar Dikko Umar Radda ya ci gaba da jajircewa wajen ganin alhazan jihar sun gudanar da aikin hajjin ba tare da wata matsala ba.

 

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito babban daraktan ya bayyana cewa hukumar ta fito da wani shiri na wayar da kan alhazai kan yanda zasu gudanar da aikin hajjin cikin nasara.Haka kuma ya bukace su da su yi addu’ar zaman lafiya a jihar da Nijeriya baki daya yayin aikin hajji a kasa mai tsarki.

 

Dankama ya kara da cewa, an hada maniyyatan ne a rukuni kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta umarce su domin samun saukin gudanar da bizar tasu.

 

Dankama ya bayyana cewa za a ilmantar da maniyyatan da za su yi aikin Hajji a kan dokokin kasar Saudiyya na maniyyata, Dankama ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin malamai daga kowace karamar hukuma 34 na jihar domin tallafa wa maniyyatan. 

 

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta tanadi masaukin da ya dace domin jin dadin mahajjatan yayin aikin hajjin na bana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci