OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yara Mata: FIDA Ta Bukaci Gwamnati Ta Bayar Da Fifiko Ga Ilimi

Yara Mata: FIDA Ta Bukaci Gwamnati Ta Bayar Da Fifiko Ga Ili

Kungiyar lauyoyin mata ta kasa da kasa, FIDA reshen jihar Imo, ta bukaci gwamnati a dukkan matakai da su samar da matakan da za su kara tabbatar da kare hakkin ‘ya’ya mata.

Kungiyar ta kuma jaddada bukatar samar da tsare-tsare da dokoki da za su bai wa kowace ‘ya mace damar samun ilimi mai inganci da ba tare da tsangwama ba, tare da kula da lafiyar su.

Shugaban kungiyar, Ndidi Anike ta kiran a wajen bikin ranar yara mata ta duniya ta 2022, wanda aka gudanar jiya.

 Da take yi wa daliban makarantun birnin Owerri jawabi kan muhimmancin ranar, ta ce, a ya kamata a bayar da  muhimmanci ga magance yawaitar tashe-tashen hankula a cikin gida, auren kananan yara, rashin daidaito da cin zarafin ‘ya’ya mata.a

Dangane da rikicin cikin gida, mataimakiyar shugabar kungiyar, Dokta Chizo Okpara ta ce FIDA ta himmatu wajen taimaka wa mata da yara da suke fuskantar cin zarafi don samun

Ta ce kungiyar za ta hada kai da dukkan mahukuntan makarantun jihar don tabbatar da cewa an samu rahoton rashin adalci da aka yi wa kowane daya daga cikin daliban domin ci gaba da hukunta wadanda suka aikata laifin.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci