OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kama Masu Garkuwa Da Mutane 9 Da Kashe 2 a Bauchi

'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kama Masu Garkuwa Da Mutane 9 Da

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wasu mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da kashe wasu biyu.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ceto mutum daya a samamen da suka kai kauyen Maina Maji da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakil ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Bauchi.

Wakil ya ce rundunar ‘yan sandan jihar tare da hadin gwiwar wasu ‘yan banga ne suka kai samamen.

A cewarsa, wadanda ake zargin a yanzu haka suna tsare, da sunayen su kamar haka: Ali Ibrahim dan shekara ashirin (20), "Manu Abdullahi (30), Damina Musa (22), Yusuf Mohammed (32), Buba Abdu (25), Buba Sulaiman (22), Isah Manu (25) da Suleiman Yusuf (46).

Wakil ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amince da aikata laifin da kan su ba tare da tirsasawa ba. 

Ya kara da cewa a yayin samamen, jami’an sun samu nasarar ceto wani dattijo mai shekaru 70 da haihuwa mai suna Alhaji Samaila.

A halin da ake ciki dai an samu nasarar kwato babura hudu a yayin samamen.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci