OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

FRSC ta tabbatar da anyi garkuwa da jamian ta biyu

FRSC ta tabbatar da anyi garkuwa da jamian ta biyu

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ebonyi ta tabbatar da wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatanta biyu a hanyar Abakaliki zuwa Enugu. 

 

A yan kwanakin nan an samu matsalar tsaro sanadiyar yan bindiga da suke sace mutane da suka addabi wasu hanyoyi a yankuna Nkalagu daka Ebonyi da Idodo dake Enugu.

 

Henry Igwe, babban kwamandan hukumar FRSC a Ebonyi, ya shaidawa manema labarai a Abakaliki a ranar Talata cewa anyi garkuwa da jamian biyu ne a ranar 8 ga watan Maris.

 

“ Iyalan su sun ce wasu sun tuntube su sun ce su masu garkuwa da mutane ne kuma suna neman kudin fansa.

Tattaunawar ta kasance tsakanin iyalai da masu garkuwa da mutane kuma a hukumance muna yin iya kokarinmu,” inji shi. 

 

Hakazalika, a safiyar yau Talata wasu ‘yan bindiga sun kai hari a sakatariyar karamar hukumar Ilejemeje da ke Eda-Oniyọ a jihar Ekiti, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi a tsakanin ma’aikatan. 

 

‘Yan ta’addan wadanda aka ce sun fito ne daga kauyen Obbo-Ayegunle da ke makwabtaka da Jihar Kwara, sun mamaye sakatariyar, inda suka yi ta harbin harsasai suka tilasta wa jami’ai tserewa kuma daya daga cikinsu ya samu rauni a harin." 

 

 ‘Yan ta’addan sun lalata ginin sakatariyar har yanzu ba a san musabbabin harin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rahotannin dai sun dade ana rikici a kauyukan biyu saboda matsalar fili. 

 

An dauki tsawon sa’o’i da dama ana dauki ba dadi kuma wadanda lamarin ya rutsa da su sun samu munanan raunuka kuma an kai shi Asibitin kwararru na jihar da ke Iye-Ekiti domin samun agajin gaggawa. 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci